Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya ce tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu ya san cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na tafka kura-kurai amma ya yi shiru.
Mr Saraki ya bayyana haka ne a wani martani da ya yi wa Mr Tinubu, wanda ya zargi Sanata Saraki da fcewa daga jam’iyyar APC saboda bukatu na kashin kansa.
“Na sha ganawa da Tinubu lokacin da yake jagorantar kwamitin sulhu na APC inda na yi masa korafi kan wa. Zan iya tunawa cewa a ko da yaushe shi da kansa yana korafi kan salon tafiyar da mulkin gwamnatin nan. Ya ce shi kan sa gwamnatin da ya yi fafutikar ganin ta ci zabe ba ta mutunta shi.
previous post